Gwamnatin jihar Kano Ta Ceto Wasu Yara 4 Daga Masu Fataucin Yara

Alfijr ta rawaito gwamnatin jihar Kano ta mika wa wasu iyaye hudu ya’yansu, wadanda aka sace su daga jihar Kano zuwa jihar Lagos wato (SAFARA)

Alfijr

Da yake jawabi yayin mika yaran ga iyayensu a madadin gwamnatin jihar Kano, sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya ce hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce ta ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

SSG ya bayyana sunayen wadanda abin ya shafa da Sama’ila Sabo, 12, Umar Muhammmad Sani, 12, Isah Yunusa, 13 da Abdullahi Yahaya, 14.Ya karayi nuni da cewa gwamnatin jihar Kano ba ta hakura da burinta na gano duk wasu yaran da aka sace ba bisa ka’ida ba daga hannun iyayensu aka kai su wasu jihohi.

Alfijr

Ya kuma sake bayyana cewa, kuka da zanga-zangar da mutane ke yi cewa gwamnati ta yi watsi da lamarin ba gaskiya ba ne,zance ne maras tushe, muna kokarin ganin mun ceto yaran tare da hadin kan iyayensu.

Kano na daya daga cikin jihohin Najeriya masu zaman lafiya da tsaro. Na tabbatar muku cewa nasarar da aka samu ba ta a zo a gani ba ne, sai dai saboda alkawurran da gwamnati ta yi da kuma kokarin da take yi” inji shi.

Alfijr

Ya yi bayanin cewa gwamnati ta tsaya tsayin daka, don tabbatar da tsaro a jihar ganin cewa galibin manyan titunan da aka da su gwamnati ta Samar (CCTV) don sanya ido kan zirga-zirgar mutane da ababen hawa, dabbobi da nufin dakile laifuka da aikata laifuka a jihar.

Usman Alhaji, ya tabbatar wa da iyayen yaran cewar gwamnati zata duba abin da zata ba su domin kara zage damtse wajen kulawa da iyalan nasu, ya bukaci jama’a da su hada kai da juna domin tabbatar da zaman lafiya a Kano.

Alfijr
Tun da farko, shugaban kwamitin aiwatar da bacewar mutanen Kano, Mai shari’a Wada Rano (Mai Ritaya) ya ce kwamitin ya samu nasarar ceto yara 14 da aka yi safararsu tun kafuwarsa.

Ya bayyana cewa an sace yaran hudu ne a lokacin da suke sayar da abin rufe fuska a wani wuri a jihar.

Mai shari’a Wada Rano ya yi kira ga iyaye da su ji tsoron Allah su guji jefa rayuwar ‘ya’yansu cikin hadari.

Ya ci gaba da cewa kwamitin yana aiki tukuru domin ganin ya cika aikin da aka dora masa. Ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa amincewar da kwamitin ya samu.

Slide Up
x