Gwamnatin Jihar Kano ta Amince Da fitar Da kudin fiye Da Naira Miliyan Casa’in da bakwai domin biyan Wadanda Suka Mallaki Gidaje a wurin da Za’a gina Ofishin Yan Sanda a Unguwar Dorayi Karama dake karamar hukumar Gwale.
Alfijir labarai ta ruwaito shugaban rikon karamar hukumar Gwale, Alhaji Abubakar Mu’azu Yusuf Mojo ne ya bayyana hakan a jiya Laraba lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Mojo, Yace tini aka Biya mamallakan wadanda Gidaje kudaden su, kuma nan bada Jimawa ba Za’a Fara aikin Gina Ofishin Yan Sandan, domin kawo karshen matsalar rashin tsaro tare da tabbatar zaman lafiya a yankin.
Shugaban karamar hukumar Yace, sun yi nasarar gyara motocin Jami’an Tsaro a karamar hukumar ta Gwale duk da nufin inganta harkokin Tsaro a yankin.
Ya godewa Gwamnan Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo bisa yadda suke nuna kishin karamar hukumar ta Gwale dama Jihar Kano baki daya.
Shugaban ya Kuma yabawa shugabannin jami’an tsaron yankin, bisa irin Jajircewarsu, yana mai Kira ga Alummar karamar hukumar su bada hadin kai da goyan baya ga jami’an tsaron domin cimma nasara.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj