Gwamnatin Kano ta Bada Sabuwa Sanarwa Ta Musamman Ga Ma’aikatan Jihar

IMG 20240112 WA0302


Gwamnatin jihar kano tace ta rage lokacin aiki ga ma’aikatan ta a fadin jihar a cikin watan azumin Ramadan mai alfarma.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ofishin shugaban ma’aikata ya fitar mai dauke da sa hannun babban Sakataren Ofishin Umar Muhammad Jalo, wacca kuma aka aikewa dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.

Sanarwar tace gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ne ya amince da wannan matakin domin saukakawa ma’aikatan don su sami damar gudanar da ibadar azumin watan Ramadana cikin sauki.

Sanarwar dai tace daga ranar litinin ma’aikatan gwamnatin jihar Kano zasu rika tashi daga aiki ne da misalin karfe 3 pm na yamma maimakon karfe 4 da aka saba, amma kuma hakan ya shafi ranakun litinin zuwa alhamis ne Kawai ita kuma Juma’a tana nan a yadda take.

Gwamnan ya bukaci ma’aikatan da su yi amfani da lokacin wajen yin ibadu da kuma yiwa jihar kano addu’o’in samun zaman lafiya da cigaba mai dorewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *