Gwamnatin Kano Ta Bayyana Yi Wa Ganuwar Jihar kwaskwarima

Alfijir Labarai ta rawaito a yunkurin da take yi na dawo da kyawun ganuwar Kano kamar yadda hukumar kula da kayan tarihi ta kasa ta ayyana ta a matsayin wurin tarihi, gwamnatin Kano ta tsara yin kwaskwarima ga ganuwar da ke tsohon birnin Kano ta hanyar amfani da baraguzan ganuwar da aka rusa, in ji sanarwar.

Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki wurin ganuwar da aka rusa.
Ya kara da cewa za a amfani da “baraguzan ganuwar da aka rusa wajen sake gina ta kuma ba a bukatar mutanen da ba su da nasaba da aikin halartar wurin da aka rusa sannan an bai wa ‘yan sanda da jami’an hukumar taro ta Civil Civil Defence Corps (NSCDC) umarnin zuwa wurin domin kare shi daga masu kutse”.

Hukumomi za su dauki mataki kan duk wani “mai kunnen-kashi” da aka gan shi a wurin.

Tun bayan shan rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soma rusa wuraren da ya ce gwamnatin da ta gabata ta gina ba bisa ka’ida ba,.

Gwamnan ya zargi gwamnatin mutumin da ya gada, Abdullahi Umar Ganduje, da sayar da filaye da bayar da umarnin gine-gine ba bisa ka’ida ba, ciki har da filayen makarantun gwamnati, asibitoci, makabartu da sauransu.

Sai dai tsohon Gwamna Ganduje ya sha musanta cewa ya aikata ba daidai ba, yana mai karawa da cewa Gwamna Yusuf bai san aikinsa ba.

kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai Ga Gwamna Abba Gida Gida ya wallafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *