Gwamnatin Kano Ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

 A safiyar Juma’a ne gwamnatin jihar Kano ta sake rufe harabar ofishin Barr. Nureini Jimoh , SAN, Lauyan da ke wakiltar Sanata Ibrahim Shekarau ya jagoranci bangaren jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a wata shari’a a Abuja. 

Solacebase ta ruwaito cewa an kulle ofishin Lauyan ne a ranar Laraba bayan da jama’a suka koka kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na rufe ofishin lauyan da safiyar Laraba, bisa zargin cin hayar gida. 

Sai dai wasu da dama daga cikin mazauna yankin na danganta matakin da koma bayan hukuncin da bangaren Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC ya yi a Abuja ranar Talata inda Barista Nurieni Jimoh ya jagoranci tawagar lauyoyin da suka wakilci bangaren Sanata Ibrahim Shekarau da suka yi nasara a karar. 

Sai dai hukumar kula da filaye ta jihar Kano a ranar Alhamis din da ta gabata ta musanta cewa ta rufe ofishin lauyan, inda ta yi nuni da cewa an rufe gaba dayan ginin ne saboda rashin biyan kudin hayar Fili. 

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na ofishin Kano Murtala Shehu Umar ya sanya wa hannu, ta ce gwamnatin jihar ta rufe wasu kadarorin ne kan cajin filaye. 

Kwamitin ya bayar da sanarwar bukatar mai wannan kadarar a ranar 14 ga Satumba, 2021 sannan kuma ta aika masa da sanarwar gargadi bayan wata guda tare da tunatar da shi da ya zo ya biya hayar filin da bai biya ba daga 2016 zuwa 2021.

 Kamar yadda Hukumar da ke kula da filaye bayyana mana, ya nuna cewa kadarorin da ke fili C14/C16 na Isiyaka Rabi’u ne Ba Barista Nuraini Jimo ne ba. 

Damuwar mu ita ce mai gidan ba wanda ke hayar kadarar ba. 

A bisa wannan ne hukumar kula da filaye ta jihar Kano ke kira ga masu kadarorin da su zo su daidaita kudin filayensu, in ji sanarwar.

Slide Up
x