D P O Ibrahim Aliyu na rundunar ‘yan sanda ta Fugar a karamar hukumar Etsako ta tsakiya a jihar Edo, ya shaki iskar yanci daga hannun masu garkuwa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa bayan kama wasu da ake zargi da yin garkuwa da su, jami’an ‘yan sanda a karkashin CP Philip Aliyu Ogbadu sun kai dauki tare da tabbatar da ‘yancin Ishaq.
An yi garkuwa da Ishaq, a kusa da kogin Ise a kan tsohon titin Auchi – Ekperi- Agenebode a jihar Edo a makon jiya.
Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan dan sandan domin biyan kudin fansa N50m CSP Ishaq kafin a tura shi Edo shekaru da suka gabata, ya rike mukamin DPO a sashin ‘yan sanda na Dakata a jihar Kano.
Best Seller Channel