Gwamnatin Kano Ta Shirya  Aiwatar Da Zaben Kananan Hukumomi nan bada dadewa ba.

FB IMG 1719671782992

Gwamna Abba Kabir ne ya bayyana haka yayin taro na musamman da  shugabannin jamiyyar NNPP na kananan hukumomi 44 a gidan gwamnati.

Alfijir labarai ta ruwaito da yake jawabi a wajen taron, gwamna ya ce gwamnati tana shirye-shiyen gudanar da zaben kananan hukumomi arbin da hudu domin tabbatar da romon dimukraddiyya ya isa ga aluma na kasa.

Ya bukaci shugabannin  Jam’iyya da su kara jajircewa wajen kyautatawa yan Jam’iyya da sauran al’uma domin daga darajar jamiyyar baki daya.

Da ya juya Kan batun bawa kananan hukumomi yancin gashin kansu, gwamnan ya ce tuni dama gwamnatinsa ta bawa kananan hukumomin jihar nan yancin gudanar da shugabanci ba tare da tsangwama ba.

A nasa bangaren shugaban jamiyyar NNPP Dr. Hashim Sulaiman Dungurawa ya bada tabbacin cewa jamiyyar NNPP ce zata yi nasara sakamakon irin ayyukan alkhairin da gwamna Abba Kabir Yusuf yake aiwatar wa a jihar Kano.

A nasa jawabin, bai bawa gwamna shawara Kan al’amuran siyasa Alhaji Sunusi Sirajo Kwankwaso ya ja hankalin  shugabannin kananan hukumomi da kada suyi amfani da yancin gashin kai wajen wawashe dukiyar talakawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *