Gwamna Abba Kabir ya ce girma da darajar Bichi a masarautar kano ta sa tasa bai dawo da Sarkin Bichi ba.
Alfijir labarai ta ruwaito Abba Kabir ya bayyana hakan ne yayin wani taro na masu ruwa da tsakin jam’iyyar NNPP na kano a gidan gwamnatin jihar.
A baya dan sarkin kano shi ake nadawa a matsayin hakimin Bichi hakan tasa bayan rusa masarautun suka bar ta a matsayin da take da shi tun asali.
”Ita Bichi tana da muhimmanci sosai ga masarautar kano , saboda muhimmancinta ba kowanne mutum ake kaiwa ya zama hakimi ba, dole sai dan sarki, don haka ba mu dawo da ita ba muka bar ta yadda tarihi ya nuna”.
Gwamnan yayi fatan Sarki Sanusi II zai tura mutum mai kima da zai rike kasar Bichin a matsayin hakimi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj