Gwamnatin Kano ta shirya taron wayar da kan mata masu ciki kan shayar da nono ga jarirai wata 6, ba tare da ruwa ba

1002440317

Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Camarde Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagoranci shirya shirin karkashin tallafin mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf.

An gabatar da shirin ne a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano, wanda a ƙalla mata masu ciki sama da dari 3 ne, suka samu damar halartar taron.

Waiya ya bayyana irin yadda gwamnan Kano ya maida hankali kan lafiyar al’ummar jihar musamman masu juna biyu, tare da samar da abubuwan more rayuwa wanda lafiyar take buƙatar.

Don haka Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf yaga dacewar a kara wayar da kan mata masu ciki domin kara kula da lafiyar su da abinda ke cikinsu, ta wajen zuwa awo da kuma idan an haihun a kalla a sami wata shida ana shayar da jarirai zallar nono ba tare da ruwa ba, domin shi kansa nonon kaso kusan 70, ruwa ne, sai kuma ragowar sauran sinadarai da Allah ya tanadar domin kariya ga jariran.

Kwamishinan ya ƙara da cewar masa sun tabbatar da cewar ruwan da ake bawa jarirai yafi karfin lafiyar su, shi yasa ake yawan samun cututtuka na damun jarirai a dinga kalawa wasu abubuwan, bayan ga dalilin, wanda za ku shaida lafiyar yaron da aka bawa Ruwa da wanda ba a bawa ba ma ta bambamta.

Don haka gwaman ke kara jan hankalin iyaye mata da maza da a tabbatar da an bi wannan hanyar ta shayarwa wata shida ba ruwa, za a samu cikakkiyar lafiya da saukin kashe kuɗin siyan madara.

A nasa bangaren Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll wanda ya sami waklicin Ɗan Kadan Kano Dr Bashir Ibrahim Muhammad ya kara yabawa gwamnatin jihar Kano kan yadda gwamna Abba Kabir yake kara jajircewa akan kula da lafiyar al’ummar Kano.

Sarkin ya ja hankalin mata kan cin abinci mai gina jiki tun kafin a haihu wanda wannan zai taimakawa yaron tun kafin zuwa duniya da bayan zuwan sa. Ya kuma kara kira da mata su maida hankali zuwa wajen awo, wannan zai taimakawa uwar da abinda yake cikinta domin su zauna lafiya.

Taron ya sami halartar wakiliyar Kwamishinan lafiya na jihar kano da wakilin shugaban asibitin kwararru na Murtala Muhammad da sauran manyan likitoci da masu ruwa da tsaki a fannin lafiya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *