Gwamnatin Kano Ta Yaba Da yadda Yan Kwangila Suka Fara Rarraba Abincin Shan Ruwa A Kano
Hakan na kunshe ne cikin tattaunawar da Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam yayi da manema labarai yayin rangadin ganin kwakwaf na yadda aka fara rabon tallafin abincin shan ruwa da gwamnatin Kano take yi duk shekara.
Yayin zagayen mataimakin gwamnan na tafe da kwamishinan yaɗa labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, da sauran mataimaka na mataimakin gwamnan da kuma ƴan jaridu
Mataimakin gwamnan ya nuna godiyar sa ga Allah na yadda idon sa ya gane masa abubuwa masu kyau yayin fara zagayen gani da ido na yadda wadanda aka bawa wannan amanar aikin suka yi.
Kwamared yace an ware santoci guda 91, kowace santa kuma za a kai abincin mutum 1000, amma saboda saukaka abubuwan da kuma faɗada su wasu ƙananan hukumomi sun nemi a shigo da wata santa yadda zai ka sance 500, guda biyu, a nan ayi sannan a matsa gaba can ma ayi 500, domin rage cunkoso, wanda ya zama kowace santa zaa kai mata abincin mutum dubu 1000, sau 91, ya kama mutum dubu casa’in da daya ne zasu ci abinci ciyar war daga nan har karshen azumi.
Wannan shine tsarin da gwamnatin Kano tayi wanda ya kunshi shinkafa da nama ko kwai da ruwan sha, duk wanda aka saka yayi mun gansu.
A gaskiyar magana mun san da matsala sosai wanda da yawa mutane basu da abin da zasu yi buda baki, wallahi don haka mai girma Gwamnan Kano ya bada himma wajen wannnan aikin alheri
Don haka Gwamna yake kara kira ga masu hannu da shuni wajen irin wannan tallafin, iya kar abinda zaka iya koda mutum daya ne, shi ne muke kira ga bayin Allah musamman yadda kungiyoyi da masu hannu da shuni irin su Dangote da suka taimaka a ba ra, muna kira da su kara taimakawa a bana ma fiye da yadda suka yi a baya.
Muna kira da al’ummar jihar Kano da su dage da yiwa jihar addu’a da kasa a cikin wannan watan na Ramadan, su kuma yiwa gwamnan Kano addu’a Allah yayi riko da hannunsa wajen kawowa jihar ci gaba.
Insha Allah idan muka tashi tsaye akan matsalar tsaro da sauran bukatu Allah zai kawo mana cigaba, haka zalika muna mika godiya ga masu yaɗa labarai da irin kokarin da suke yi wajen wayar da kan al’umma.
Allah ya karbi ibadunmu Allah ya taimaki Kano da al’ummarta Allah ya taimaki Najeriya da sauran Musulmin Duniya baki daya Ameen




Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ