Gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa ba za ta sanar da wuraren sayar da shinkafar dubu 40 ba

FB IMG 1722327197513

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma na kasa, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta bayyana wuraren da za a sayar da Shinkafar da ta karyar da farashin ta zuwa Naira dubu 40 ba, saboda gudun ka da masu kudi su je su saye.

Alfijir labarai ta ruwaito ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema ranar laraba a Abuja.

Idris ya ce wannan shiri na daya daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta fito da su domin saukakawa yan kasa tsadar rayuwa.

Sai dai da yake magana a ranar Laraba  ministan ya ce ana shirin raba buhunhunan shinkafar zuwa jihohin Nigeria.

Ya kara da cewa, ba za a iya bayyana wuraren da za a sayar da su a fadin kasar nan ba saboda dalilai na tsaro, kuma don tabbatar da cewa talakawa da akai tsarin don su sun sami shinkafar.

“Zai yj wahala a ambaci wuraren da za a sayar da Shinkafar saboda dalilan tsaro.

“Amma muna da shinkafar a kasa, kuma za a sayar da ita a kan N40,000.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *