Gwamnatin tarayya ta amince da cire jami’o’i da sauran manyan makarantun kasar nan daga cikin hadakar ma’aikata da tsarin biyan albashi (IPPS), wanda hakan ya baiwa makarantun damar tunkarar matsalar albashin ma’aikatansu a cikin gida.
Alfijir labarai ta rawaito majalisar zartaswa ta tarayya ce ta ba da amincewar ba da izinin a zamanta na ranar Laraba a fadar shugaban kasa ta Villa Abuja.
Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai na fadar gwamnati bayani tare da wasu ministocin sakamakon taron FEC, ya kuma ce hakan ya fara aiki nan take.
Ya ce FEC ta dauki matakin cire cibiyoyi daga tsarin ne saboda damuwar da ta ke da shi na inganci da kuma kula da cibiyoyin.
A cewarsa, baya ga adawa da tsarin biyan albashi da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi, batun IPPS ya dauki lokaci mai tsawo ga mataimakan shugabannin jami’o’in, “wanda ya jawo managarcin gudanar da cibiyoyin.
Ministan ya bayyana cewa, a matsayinsu na dokoki na manyan makarantun, kamata ya yi a bar su su rika cin gashin kansu.
Idan zaku tuna cewa Kungiyar Ma’aikatan Ilimi ta Jami’o’i ta koka da rashin ingancin IPPS tare da ba da shawarar yin amfani da Tsarin Ba da Lamuni na Jami’a (UTAS) da Tsarin Biyan Ma’aikata na Jami’o’i (UP3S) don biyan albashi ga ma’aikata a manyan makarantun.
UTAS tsarin biyan albashi ne da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kirkiro domin biyan albashi da alawus-alawus na malaman jami’o’i.
Kwamitin hadin gwiwa na kungiyar ma’aikatan jami’o’i da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (JAC) ne suka kirkiro UP3S don wannan manufa.
IPPIS wanda a watan Oktoban 2006 gwamnati ta dauka a matsayin daya daga cikin Shirye-shiryenta na gyarawa, don dakile cin hanci da rashawa kamar biyan albashi ga ma’aikatan bogi, kamar yadda aka ce ya taimaka wajen kusan kashi 75% na matsalolin da suka shafi tsarin jami’o’in Najeriya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp