Gwamnatin Najeriya za ta mayar da shalkwatar FAAN zuwa Legas

IMG 20240119 003937

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta mayar da shalkwatar hukumar kula da filayen jiragen saman ƙasar (FAAN) zuwa birnin Lagos

Alfijir labarai ta rawaito Matakin na ƙunshe cikin wata sanarwa da babbar daraktar hukumar Misis Olubunmi Kuku ta fitar.

Sanarwar ta ce ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar ne ya bayar da umarnin ɗauke shalkwatar hukumar ta FAAN daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa birnin Legas da ke kudu maso Yammacin ƙasar.

Matakin na zuwa ne yayin da a farkon makonnan Babban Bankin ƙasar CBN ya sanar da ɗaukar matakin mayar da wasu sassan bankin zuwa birnin na Legas.

FB IMG 1705621151736
📸 FAAN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *