
Alfijr ta rawaito gwamnatin tarayya ta ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kwato dala biliyan 1 na kudaden da aka wawashe zuwa yanzu.
Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin jihar bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A cewar Malami, an tura kudaden da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da rage radadin talauci.
Ya kuma cewar majalisar ta amince da sabon daftarin dabarun yaki da cin hanci da rashawa domin karfafa yaki da rashawa a kasar.
Yayin da ya ke bayyana damuwar gwamnati kan al’amuran da suka shafi kasafin kudi, wanda ya bayyana a matsayin abin damuwa, ya kara da cewa za a binciko duk wani matakin da ya dace don magance shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ