Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Yanke Wa Mutum Wuta Ba Tare Da Sanarwar Kwanaki i 10 Ba

Alfijr ta rawaito hukumar Kare hakkin mai saye da Mai sayarwa ta Tarayya, FCCPC, ta ce haramun ne a yanke wa mutum wuta ba tare da bashi sanarwa ta kwanaki goma da ga ranar da a ka aiko masa da takardar biyan kuɗi ba.

Mataimakin Shugaban Hukumar Babatunde Irukera ne ya bayyana haka a jiya Laraba a Calabar, a wani dandalin warware korafe-korafen masu amfani da wutar lantarki.

Alfijr

Irukera ya koka da yadda Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Fatakwal, PHED, ke yi a Calabar da kewaye.

Ya ce daga binciken da hukumar ta yi, PHED ba ta yi wani abin azo a gani ba wajen samar da wuta ga al’umma daidai da kudaden da kamfanin ya caje su ba.

Hakan ne ya sanya Irukera ya ayyana ayyukan kamfanin rarraba wutar lantarki na Cross Rivera a matsayin “zalunci”.

Alfijr

Ya ce rahotannin da suka samu kan al’amura da dama sun hada da yanke wa jama’a wuta da kamfanin ke yi ba tare da bin doka ba.

“Yawan yanke wutar al’umma saboda bashi ba wai kawai bisa ka’ida ba ne, abin takaici ne da kuma cin zarafin jama’a.

Yanke wa al’umma wuta ba bisa ka’ida ba zalunci ne,” in ji shi.

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa