Zamu ɗauki ma’aikata Kusan Dubu 300,000 aikin yi a fadin kasar nan Domin Ganin kasarmu ta zama wuri mafi Aminci.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar dake kula da Yaƙi da yaduwar ƙananan makamai ta ƙasa (NATCOM) tace ta kammala shirye-shiryen ɗaukar aiki da horar da ma’aikata Kusan Dubu 300,000 a fadin Tarayyar ƙasar nan Domin dakile yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba.
Mukaddashin Darakta Janar na NATCOM, Otunba Adejare Rewane Adegbenro, Wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a jiya Lahadi Yace adadin ma’aikata kusan 7,000 ne zasu yi aiki a kowace jiha ta Tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Yace, “Zamu ɗauki ma’aikata Kusan Dubu 300,000 aikin yi a fadin kasar nan Domin Ganin kasarmu ta zama wuri mafi Aminci.
“Ba za mu yi aiki kawai ba, duk za su sami horo mai inganci. Shi kansa wannan kuma zai rage yawan marasa aikin yi a kasar. Zamu haɗa karfi da karfe da Sauran jami’an tsaro wajen tafiyar da kwas din mu.”
“Game da ɗaukar ma’aikata 7000 a Kowace jiha, masu sha’awar su sa ido kan ka’idojin jaridun kasa. Amma abu ɗaya ya tabbata, Muna neman matasa masu kuzari Don horarwa.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Thanks god
Update news