Halin firgici: Wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja ya kauce hanya a Kaduna

IMG 20240527 WA0178

Daga Aminu Bala Madobi

An shiga halin dar-dar yayin da wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja ya kauce daga kan hanyar layin dogo a hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Lahadi.

Alfijir labarai ta ruwaito Jirgin wanda ya dauko fasinjoji da dama ya taso Kaduna da misalin karfe 8:05 na safe amma ya kauce hanya a Jere bayan kimanin awa daya.

Sanata Shehu Sani, wanda ya taba wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana cewa, “wani karamin jirgin kasa na Abuja, Kaduna a wannan rana ya kauce hanya daga Jere, amma injiniyoyi sunyi kokari kawo dauki.”

Kimanin shekara daya da ta gabata ne Sanata Sani shima ya sanar da cewa an sake samun matsala a hanyar.

Akan haka ya yi kira ga hukumar kulada tashoshin jiragen kasa ta Najeriya NRC da ta gaggauta tabbatar da tsaron lafiyar fasinjojin jirgin da suka makale.

Sani ya rubuta cewa: “Tsarin jirgin Kaduna Abuja ya lalace; NRC don Allah a tabbatar da tsaro da amincin fasinjojin da suka makale.”

Yayin da babu wata sanarwa a hukumance daga Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), jami’an tsaro da suka hada da jami’an ‘yan sanda da na Sojoji na nan a kasa domin bayar da tallafi, yayin da wasu motoci kusan uku suka tashi daga kan hanya don bayar da tallafin gaggawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *