…Abin Mamaki Ko Abin Ban Haushi?
Daga Barr. Badamasi Suleiman Gandu
Kan muhawarar dake cigaba da yamutsa hazo a siyasar Kano dangane da zargin cin hanci da rashawa da ake zargin daraktan kula da harkokin gwamnan jihar Kano ya haifar da zazzafar muhawara.
Yayin da wasu ke ganin da cewar, a daidai wannan mataki a dakatar da irin wannan tattaunawa, Kuma yawan cin hanci da rashawa a rayuwarmu ta siyasa ya sa shiru kusan ba zai yiwu ba.
Idan ana maganar cin hanci da rashawa a Najeriya, watakila tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje bai da bakin magana, shi ne mafi rauni da za iya cewa baida ta cewa, kuma mutum mafi karancin aminci da za a iya yadda da sahihancin amanar sa kan kyawawan dabi’u a wannan sabga. Saidai ba zato ba tsammani, kwatsam sai aka jiyo tsohon Gwamnan yana babatu a matsayin mai rajin yakar batun, duk da kaurin suna da yayi a lokacin gwamnatin sa na cin hanci da rashawa, Shin abin mamaki ne ko kuma mafi muni, ko abin ban tsoro?.
Shekara takwas kenan Ganduje yana mulkin jihar Kano cikin zulumin badakalar zarge zarge na cin hanci da rashawa da yayi masa kanta. Daga faifan bidiyon dala da ya karade ko ina a duniya, zuwa zarge-zargen da ake yi a kan dangin sa, abin kunya da muni da ya fi bayyana a wa’adin mulkinsa. Hakika tarihi zai tuna cewa babban dan sa ya kai Uwargidan sa, matar Baban sa (mahaifiyarsa) a gaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) bisa zargin almundahana. Irin wannan nuna son rai ga iyali, hakan bai taba faruwa ba a tarihin siyasar Kano.
Hatta wa’adin da Ganduje ya yi a matsayin shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa ya zo da cece-kuce, a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa zargin cin hanci da rashawa ne ya sa aka gaggauta tilasta masa yin murabus. Idan aka yi la’akari da wannan tirka tirka, mutum zai iya sa ran cewa batu ne mai cike da almara, Maimakon haka, Tsohon Gwamnan cikin babbar murya yana zargin gwamnatin Kano me ci, har yake kiran su da cewa “barayi ne daga sama har kasa,” yayin da ya umurci abokan siyasar sa da su cigaba da tona musu asiri.
Wannan magana ita kadai ta ci amanar siyasar da ke tattare da fallasa kuma tana nuna tsantsar munafunci da mancewa da irin badakalar zarge zarge masu muni da akaiwa Gwamnatin sa abaya wanda karara kowa ya gani.
“Duk da kwararan hujjoji, musamman kan bidiyon dala, na yi amfani da kalmomi kamar “zargin” ko “Wanda ake zargi.” A matsayina na lauya, ina bin sashi na 36(5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara), wanda ke ba da tabbacin cewa hakan babu laifi. Amma kai tsaye ka ambaci sunan wani karara a matsayin barawo, kamar yadda Ganduje ya yi, ba wai batanci ba ne kawai, a’a, rikon sakainar kashi ne da rashin bin tsarin mulki.
Har ila yau, ya kamata a tuna cewa a lokacin gwamnatin Ganduje, an hana zababbun shugabannin kananan hukumomi, mataimakan shugabanni, da kansiloli da suka cancanta kudaden su. Aka karkatar da kudaden da aka tanadar musu. In banda a kwanakin baya ne Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya gaje shi ya takarkare ya biya mazan kudin da ya gada har zunzurutun kudi naira biliyan 16, duk da cewa wadanda suka ci gajiyar wannan tagomashi ba su yi aiki a karkashin gwamnatin Abba Gida Gida ba, ballantana su yi tarayya da tsarin siyasar sa. Wannan kokarin sauke nauyin bai ɗaya yana nuna tsantsar mutuntawa, gaskiya, tausayi da sanin Girman Dan adam ayayin gudanar da mulki.
Don haka, tambayar ita ce kai tsaye: tsakanin gwamnatin da ake zargi da rike kudade da kuma wata gwamnatin da ta zabi biyan basussukan da aka gada, aka cinye musu hakki, wane ne ke nuna alamun da gaske yake don yin magana kan cin hanci da rashawa?
A ganina, tsoma baki ba zato ba tsammani da Ganduje yayi kan batun yaki da cin hanci da rashawa kawai ba iya borin kunya bane, siyasa ce. Domin mutumin da ya dade yana facaka da dulmiya hannayensa dumu-dumu da iyalin sa cikin baitulmalin talakawa, kwatsam aka jiyo yana gabatar da kansa a matsayin dan gwagwarmaya wanda a yanzu ke rajin yakar cin hanci da rashawa – a al’adan ce, shin wai kura ce za ta ce da kare maye???
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t