Hawa Da Saukar Farashin Man Fetur Da Matatar Dangote Ke Yi Ka Iya Jefa Nigeria cikin Masharsharar Tattalin Arziki — In Ji Yan Kasuwa

IMG 222905 31126 1769894958576

Masu harkar sayar da man fetur a Najeriya, tare da masana harkar makamashi, masu sa ido da ƙungiyoyin ƙwadago, sun bayyana damuwa kan yadda ake fama da rashin tabbas na ragewa da kara farashin man fetur da kuma  rarraba sa a ƙasar.

Sun ce wannan yanayi na haifar da fargaba a kasuwar man fetur, musamman ganin yadda farashi ke sauyawa ba tare da wani  tabbatacce ba, lamarin da ke jefa ’yan kasuwa da masu amfani da mai cikin ruɗani.

Masu sa ido sun danganta matsalar da tsarin aikin da Matatar Dangote ke bi, musamman tsarin da ake kira single train.

Hakazalika Sun yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, hakan na iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.

Da suke zantawa da manema labarai, wasu daga cikin masu sayar da man fetur sun ce yadda matatar ke aiki da tsarin ragewa da kara farashin man fetur a halin yanzu bai yi dai-dai da tanade-tanaden dokar Petroleum Industry Act (PIA) ba, dokar da aka kafa domin tsara harkar man fetur da gas a Najeriya.

A cewarsu, hakan na iya girgiza tsarin samar da man fetur, tare da jefa kasuwa cikin wani hali.

Masu sayar da mai masu zaman kansu sun ce a kwanakin baya farashin man fetur daga matatar, wato farashin da ake sayarwa ga ’yan kasuwa kafin ya isa gidajen mai, ya tashi daga naira ₦699 zuwa ₦799.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *