Uwargidan marigayi General Sani Abacha, her Excellency Dr Hajiya Maryam Abacha na mika Ta’aziyyarta ga iyalan marigayi Malam Mato wanda aka fi sani da Mal Nata’ala mai sittin goma.
Haj Maryam ta kara da cewar wannan rashin ba na iya iyalansa bane, rashi ne da aka yiwa al’ummar Hausawa, duba da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen wayar da al’umma da kuma nishadantarwa a lokaci guda.
Ta kara da cewar tana kara mika gaisuwarta ga al’ummar masana’antar Kannywood na wannan rashi da aka yi musu, da fatan Allah ya yafe masa Allah ya bawa iyalansa da yan uwansa da abokan sana’ar sa hakurin wannan rashin ameen.
A Ć™arshe tayi kira da Al umma wajen dagewa da yiwa Ć™asa addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali duba da halin da ake ciki na firgici da rashin tsaro.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t