Daga Auwalu Sufi
An bukachi mawadata dake cikin AL, umma su kasance masu kulawa da ceto matasa dake daure a gidajen gyaran hali na Jihar nan.
Shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta (OON) shine yayi wannan Kiran Alokacin da ya Ke fansar wasu daurarru da, ke gidan gyaran hali na Gwauran Dutse.
Doguwa yayi dogon bayani tare da Jan hankali ga matasa da su yadda da kaddara, Kuma su cigaba da yin Addu, ar Allah ya kawo mafita musanman ma acikin wannan watan.
Hon Doguwa Wanda yake kasa Mai tsarki, ya samu wakilcin kakakin jam, iyyar Apc na Jihar kano Hon Alh Ahmed Aruwa, ya bayyana cewar Hon Alhassan Ado Doguwa ya saba zuwa duk shekara domin fitar da wadanda aka daure domin sallamar su.
Daga cikin wadanda Hon Doguwa ya sa aka sallama din sun hada da masu kanananan laifuffuka da wadanda aka yiwa tarar kudade.
Doguwa ya bada Buhunhunan shinkafa manya guda 10 da taliya katan biyar mangyada katan 5,buhun garin kwaki 2, ruwan sha leda 100, sabulu katan5, da bijiminsa da za, a yankawa mazauna gyaran gidan hali.
Doguwa ya sa an saki daurarru, da dama.
A jawabin sa mataimakin kwantorola na gidan gyara hali na gwabron Dutse Malam Kabiru Abdullahi Nassarawa, ya bayyana cewar Hon Alhassan Ado Doguwa ya saba bada irin wannan tare da fitar da daurarru da sauran Ayyukan neman Lada wadanda wasu Baza su fadabu saboda yayi ne tsakanin sa da Allah a saboda haka nema ya bayyana cewar Allah ne kadai zai biyashi saka makon,.
Daga bisani mataimakin kwantorola Kabir Abdullahi Nassarawa ya tara mazauna gidan gyaran hali na gwabron Dutse ya nuna Kayayyakin da Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya bayar, yayin da suka barke da sowa da Addu, oin Allah ya taimaki Alhassan Ado Doguwa
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD