Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa)

Screenshot 20240615 123550 Facebook

A irin wannan ranar ce 9 ga watan Zul-Hijjah, SHEKARA ta goma bayan Hijira a Dutsen Arafat (ranar Arfa kenan) Annabi Muhammad S.A.W ya yi wata huduba mai ratsa zuciya.

Fiyayyen Halitta (S.A.W) Ya fara da cewa:

“Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai
yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan
wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari
abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar
da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a
wannan wuri a yau.

🎇
Ya ku mutane kamar yadda ku ka ri’ki wannan
wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da
kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma
abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi
da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma
karewa, ku maida wa mutane kayan da suka ba
ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu
su cuce ku.

🎇
Ku tuna fa, hakika Allah zai yi
sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana
cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin
da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye
addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku
akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka
ku guji binshi akan kanana.

🎇
Ya ku jama’a hakika kuna da hakki bisa
matayenku, amma su ma suna da hakki bisa
kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su,
Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su
kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu
domin su majibintan al’amurran ku ne, kuma
mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi
abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci
zina.

🎇
Ya ku jama’a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah
(SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku
azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka.
Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi.

🎇
Ku sani fa, kowane musulmi dan uwan musulmi
ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da
fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da
aikata kyawawan ayyukka.

🎇
Ku tuna fa (ya ku jama’a) wata rana za ku tsaya
gaban Ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku,
saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da
hanya madaidaiciya bayan na kau.

🎇
Ya ku jama’a ba wani annabi ko manzo da zai
zo bayana kuma babu wani addini da zai zo
(bayan addinin musulunci), saboda haka ku yi
tunani sosai akan wannan magana da na gaya
maku, kuma ku fahimce ta (sosai).

🎇
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); (Alkur
ani) da kuma (Sunnah). Idan kun bi wannan ba
za ku taba bata ba.

Duk wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji maganata daga karshe su fi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.

🎇
Ya Allah… ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar
da aikenka zuwa ga bayinka.”

‘Yan uwa ku yada (sharing) wannan hudubar ta Masoyin mu Annabi Muhammad S.A.W ga ‘yan
uwa musulmai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *