Hukumar Alhazan Najeriya Ta Kama Alhazan Bogi Guda Biyu A Minna

FB IMG 1718460854146

A jiya Juma’a ne jami’an Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON su ka kama wasu ƴan Najeriya biyu da suka yi basaja a matsayin alhazai a sansanin Minna da ke Makkah, kasar Saudiyya.

Alfijir labarai ta ruwaito an kama alhazan bogin ne da  Abu Mahmud da Ismaila Yahaya, suna cudanya da alhazan na ainihi, yayin da su ke hutawa bayan tafiyarsu daga Makka zuwa sansanin Muna.

An gano mahajjatan jabun ɗauke da jabun katin shaida na Nusuk tare da sanya harami kamar yadda da alhazai ke sanya wa kuma su ka sake da alhazai.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa ashirin su ya tonu daga karshe kuma tuni jami’an NAHCON suka tsare su.

A halin yanzu dai jami’an hukumar ta NAHCON na ci gaba da yi wa wadanda aka kama din tambayoyi, inda daga bisani za su mika su ga hukumomin Saudiyya.

Screenshot 20240615 151404 Facebook
Minna

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *