Hukumar (FCCPC) ta sanar da wa’adin watanni guda ga ‘yan kasuwa da suke ta’ammali da farashin kayayyaki, tare da karfafa musu gwiwar rage farashin kayayyaki.
Tunji Bello, wanda shi ne sabon mataimakin shugaban hukumar FCCPC da aka nada, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kwana guda da masu ruwa da tsaki suka yi kan farashin kayyyaki wanda aka gudanar yau Alhamis a Abuja.
Bello ya tabbatar da cewar hukumar na shirin fara aiwatar da ayyuka da zarar wa’adin dakatarwar ya kare.
Ya ce, “A karkashin sashe na 155, waɗanda suka karya doka ko daidaikun mutane ko kamfanoni zasu fuskanci hukunci mai tsanani da suka haɗa da tara da dauri idan kotu ta same su da laifi.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj