Wata Sabuwar! Wani Soja Ya Harbe DPO A Jihar Zamfara

FB IMG 1724947575564

DPO din Wasagu a jihar Zamfara, SP Halliru Liman ya rasu, inda rahotanni su ka tabbatar da cewa wani soja ne ya harbe shi a shingen binciken ababen hawa a jihar ta Zamfara.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, jami’in dan sandan da ya rasu ya na kan hanyarsa ta zuwa birnin Kebbi na jihar Kebbi domin halartar taro a yayin da sojoji su ka tsayar da shi a hanyar Danmarke.

Abubakar, ya ce an kashe dan sandan duk da cewa ya nuna shedar cewa shi jami’in dan sanda ne.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yau Alhamis, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya nemi a gudanar da bincike mai zurfi kan yadda abin ya faru tare da tabbatar da an hukunta masu hannu kan lamarin.

“A ranar 28 ga watan Agusta na 2024 da misalin karfe 10:30 na safe, wani jami’in soja ya kashe SP Liman a yankin Dan Marke na karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

” Lamarin da ya kai ga kisan abin firgitarwa ne kuma baza a amince dashi ba.”

Sanarwar ta ce bayan jami’in sojan ya tsayar da DPO din ya harbe shi a kansa wanda nan take ya rasa ransa.

Daily Trust
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *