Hukumar Gidan Gyaran Hali Ta Magantu Kan Bacewar Murja Kunya A Gidan

FB IMG 1708265600330

Daga Fauziyya Momin Haidar

Hukumar kula da gidan gyara hali ta kasa reshen jihar kano ta bayyana cewa tun ranar Alhamis ta saki Murja bisa umarnin kotu.

Alfijir labarai ta rawaito Tun a daren jiya dai ake ta rade-radin an nemi Jarumar TikTok din Murja Ibrahim kunya a gidan gyaran hali an rasa ta, wanda hakan tasa Ake zantuka da korafe-korafe akai musamman a dandalin sada zumunta.

Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nassarawa ya shaidawa Daily Nigerian hakan a yau lahadi.

“Sananniyar ‘yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya ba guduwa ta yi daga gidan yari ba mu ne muka sake ta bisa Umarnin kotu” inji Musbahu Kofar Nasarawa

A cewar sa, tun ranar Alhamis takarda ta zo daga kotu don neman a sake ta, kuma gidan yarin ya sake ta tun a ranar.

Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a wajensu, kuma kotu ce ta ce su sake ta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *