Alfijr ta rawaito hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa, FRSC, reshen jihar Kogi a ranar Talata ta mayarwa iyalin wata da ta yi haɗari a jihar, kuɗi da ya kai Naira miliyan 3.2.
Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar, cewa kudin, mallakar wata Misis Beatrice Ehimare ce da ta yi hatsarin mota a ranar 23 ga watan Janairu, a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Kwamandan Sashen shiyya ta RS8.38 Gegu ne ya gabatar da kudin da aka kwato ga ɗan wacce ta yi haɗarin, David Ehimare.
Lokacin gabatar da kuɗin da aka gudanar a Lokoja, kwamandan sashin Kogi, Corps Stephen Dawulung, ya yabawa jami’an da mutane bisa jajircewarsu da kishin kasa.
“Ina so in sake jaddadawa a nan a yau cewa kudiri na ne na ci gaba da aiwatar da aikin ceton rayuka da kare dukiyoyi tare da mafi girman jajircewa, himma da mutunci wanda hukumar FRSC ta shahara da shi.
“A matsayin umarni, muna yi wa Misis Beatrice fatan samun sauki daga raunin da ta samu daga mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Litinin,” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇