Alfijr ta rawaito Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta ce an rufe titin jirgin da ke filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke Ikeja a jihar Legas na tsawon makonni takwas.
A cikin wani sakon twitter a ranar Litinin, Hukumar ta sake nanata kudurinta na aminci, tsaro da kimarta.
Za a yi amfani da hanyar taksi B-18L don duk ayyukan jirgin,” in ji shi.
Sanarwar ta kara da cewar, ana sanar da jama’a cewa an rufe titin jirgin sama mai lamba 18R/36L na filin jirgin saman Murtala Muhammed Int’l, Legas na tsawon makonni 8 don gudanar da aikin gyare gyare.
Za a yi amfani da hanyar taksi B-18L don duk ayyukan jirgin.
FAAN, ta himmatu wajen bin ka’idojinta..Lafiya, Tsaro da Jin kai. In Ji sanarwar
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai