Hukumar Kwastam Ta Kama Buhu Dubu Da Sha Biyar (1,015) Na Naman Jaki

Hoto Daily Nigerian

Hukumar yaki da fasa kwauri ta kasa, shiyya ta C ta lalata buhuhunan bushashen naman jaki guda 1, 015 da fatar Jakin a Edo.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar shiyya ta C, Jerry Attah a ranar Laraba ya ce kayayyakin wani bangare ne na wadanda aka kama tsakanin 15 ga watan Yuli da 15 ga watan Satumba a shiyyar.

Attah, ya ambato kwanturolan da ke kula da shiyyar, Michael Ugbagu na cewa an lalata fatar jakunan a kan idon sauran hukumomi.

Ya bayyana bukatar hada karfi da karfe wajen kare dabbobin daji.

Mista Ugbagu ya ce matakin nada alaka da kokarin da ake na magance haramtattun kasuwanci.

Ya ce, Nijeriya tana daga cikin kasashen da suka sanya hannu wajen haramta cinikin Jakuna.

“Hukumar kula da noma da raya karkara a shekarar 2017 ma ta hana yanka Jakuna a kasar nan domin hana karewar su.

” Amma kamar yadda kuka sani, sassan jikin jaki na da kima sosai a yankin Asia, mussaman China inda suke amfani da shi don magunguna”, inji shi.

Kwanturolan ya kuma ce, fasa kwauri na amfani da manyan motoci na alfarma wajen safarar jakunan cikin dare don kaucewa kamu.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *