Hukumar Kwastam Ta Najeriya Ta Kwace Litar Man Fetur 26,792 A Badagry

FB IMG 1719254190888

Tawagar Zone A na Operation Whirlwind Task Force, na Hukumar kwastam ta Najeriya, sun yi nasarar kwace fiye da lita 26,792 na Premium Motor Spirit (PMS) a Badagry.

Alfijir labarai ta ruwaito kwanturola Hussein Ejibunu, Shugaban rundunar ‘Operation Whirlwind’ ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Yau Litinin a Seme, Legas.

Ya ce, “Rundunar tamu da ta yi aiki da sahihan rahotannin leken asiri, ta kama bugu 43 na man fetur kowace lita 30, adadin ya kai lita 1,290.

“Mun kuma kama wata motar tanka mai lamba IMIAD3840TWO03697 dauke da lita 15,200 na man fetur a tashar mai na Jubau da ke kan titin Seme Badagry.

“A ranar 14 ga watan Yuni, mun kama wata mota kirar Suzuki mai lamba SMK 83 BK, wacce ake safarar man fetur.

“Mun kuma kama wata Pathfinder Jeep mai lamba ABJ 591 DC da Toyota Avensis guda daya mai lamba 1973, dukkansu sanye da manyan tankoki na musamman dauke da man fetur a tashar Musa.

“Duk da cewa har yanzu ba mu tantance adadin litar da ke cikin kowace mota ba, mun kuma kama wasu mai guda 124, kowanne lita 30, jimillar lita 3,720, da kuma bugu 65 na man fetur, kowace lita 40, adadin ya kai lita 2,600.”

KBC Hausa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *