Hukumar NCC Ta Magantu Kan Matsalar Kira Da Data Da Aka Samu A Najeriya

FB IMG 1710824142994

Kira da data sun dawo daidai bayan katsewar wayoyin teku.

Alfijir labarai ta rawaito hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC, ta ce an dawo da sabis din kira da na data bayan katsewar da wayoyin sadarwa su ka yi a ƙarƙashin teku.

Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Dr Reuben Muoka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Abuja.

Mista Muoka ya ce an maido da sabis din ne, biyo bayan katsewar da wayoyi su kayi a Teku a Cote de’Ivoire da Senegal a ranar 14 ga watan Maris, wanda ya haifar da matsalar kira da data.

“Muna farin cikin sanar da cewa a yanzu an maido da sabis zuwa kusan kashi 90 cikin 100 na mafi girman karfin amfani da su,” in ji shi.

Muoka ya ce dukkan kamfanonin sadarwa da matsalar ta shafa sun dauki gabaran gyara ta hanyar gyaran na karkashin ruwa ta hanyar amfani da wadanda basu katse ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *