Hukumar NDLEA ta gudanar da taron masu ruwa da Tsaki (Stakeholders)  domin magance shaye-shaye da ya addabi jihar Kano

IMG 20250505 211047

Hukumar NDLEA ta gudanar da taron masu ruwa da Tsaki (Stakeholders)  domin magance shaye-shaye da ta addabi jihar Kano

Shugaban kwamitin gudanarwa na wannan gangami Alh Ahmad Sa’idu Sufi ya ja hankalin iyaye da al’umma wajen yadda ya kamata a tunkari wannan annoba data danno kai a wannan jihar.

Ya kara da cewa wannan matsayi da aka bani dama ce da na samu domin na taimaki jahata da al’umma, kuma ina mai tabbatar da cewar zan bada duk wata gudunmawa da ta haɗa da dukiyata da lokacina domin magance wannan matsalar ta shaye shaye a wannan jiha tamu.

Alh Ahmad Sufi ya kara da cewar babban abin da ya basu karfin guiwar yin wannan jihadi bai wuce ganin yadda jihar Kano ta dawo mataki na biyu a Najeriya wajen shaye shaye ba.

Sannan kuma idan aka ce ba wannan hanyar za a biba ta jan hankalin masu yin wajen dainawa to akwai babbar matsala! Domin idan duk wanda aka kama daure shi za ayi ina mai tabbatar muku da cewar wannan Jihar bata da inda zata iya ajiye mutane.

Don haka muke bada shawarar babbar hanyar da za a bi domin magance wannan matsalar itace jan masu wannan larurar a jiki da daina kyamarsu, to idan aka ci gaba da haka da izinin Allah za a kawo karshen wannan masifar a jihar Kano.

Shima a nasa bangaren shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kano Abubakar Idris ya yabawa mahalasta wannan taro na yadda kowa ya nuna damuwarsa da bada goyon baya akan yadda za a magance wannan masifar da ta addabi jihar Kano.

Sannan kuma ya yabawa Alh Ahmad Sa’idu Sufaye na yadda duk da abubuwan da suka sha kansa amma ya yadda ya karbi shugabancin wannan kwamiti na kawo gyara kan shaye shaye a wannan jihar

Kwamandan ya bawa iyaye da yaya shawarwarin da ya kamata su bi domin samun daidaiton tarbiyya.

1. Iyaye su fahimci ta inda suka kauce wajen tarbiyyar ƴaƴansu.

2. Masu wannan shaye-shaye su gane cewar akwai babbar illa ga lafiyarsu da kuma rayuwarsu.

3. Matasa su zamo suna da manufa a rayuwarsu.

Mai bawa shugaban kasa shawara akan kafafen sadarwa Abdulaziz Abdulaziz ya bayyana yadda shugaba Tinubu ya damu akan wannan masifar don haka ya haɗa wata tawaga mai ƙarfi domin magance shaye shaye a kasa baki daya.

Wannan tawagar kuma ta sami wata babbar nasarar kame wasu kwantenoni sama da dubu uku a jihar Lagos na kayan maye.

Sannan Abdulaziz Abdulaziz yayi alƙawarin ɗaukar nauyi mawaka saka gasa wato (Challenge) akan wakokin su na gargadi akan shaye-shaye domin wannan hanyar ce sakon zai isa ga al’umma nan da nan.

Ana bangaren shugaban hukumar tace finafinai da dab i ta jihar Kano Abba El Mustafa ya yabawa shugaban hukumar ta NDLEA da Kuma Kakakin hukumar Sadiq Muhd Maita yadda suke gudanar da salon aikinsu na zamani da nuna kwarewa.

El Mustafa ya Kuma yi albishir din cewar zasu bawa masu shirya finafinai damar mai da hankalin finafinansu akan wannan matsala.

Taron da ka gudanar da shi Kano a yau Litinin ya sami halartar manya da kananan masu kishin Kano, yan kasuwa da mashawartan gwamnan Kano na musamman da yan kasuwa da sauransu.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *