Hukumar NECO Ta Sanar Da Ranar yin Rijistar Jarrabawar Shiga College Ta 2022, Da Kudin Da Za a Biya Don Rigista

Alfijir

Alfijir

Jaridar Alfijir ta rawaito, hukumar shirya jarabawar ta kasa ta sanar da fara rijistar jarrabawar gama-gari ta kasa ta 2022, domin shiga karamar sakandare ta 1 na kwalejojin tarayya.

Maga takardar hukumar NECO, Dantani Wushishi, ya sanar da hakan a wani karin haske a shafin Hukumar na yanar gizon.

Alfijir

Wushishi ya ce, an yi rijistar ne kawai ga daliban da ba za su kai shekaru 10 ba a watan Satumba na 2022.

Hukumar jarrabawar ta kasa tana son sanar da jama’a cewa rajistar jarrabawar gama gari ta kasa ta 2022 don shiga kwalejojin hadin gwiwar gwamnatin tarayya za a farata

Alfijir

Wushishi ya ce, kudin rajista Naira 4,500 ne ga kowane dalibi, yayin da ya kamata a biya a cikin asusun ajiya na NECO ta hanyar katin ATM, reshen banki, USSD, banki na intanet ko wallet,” inji shi.

Ya kuma sanar cewa za a yi rajistar jarrabawar ne a yanar gizon hikumar: www.neco.gov.ng.

Alfijir

Da yake bayyana cewa za a rufe rajistar ne a ranar 23 ga watan Afrilu, ya ja hankalin iyaye da su ziyarci yanar gizo ko duk wani ofishin hukumar NECO da ke kusa da su domin samun karin bayani kan yadda ake yin rajistar.

Slide Up
x