Hukumar Tattare Haraji Ta Jihar KanoTa Kori Daraktoci Takwas

IMG 20240119 225254

Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta sanar da korar daraktoci 8 daga mukamansu, inda ta umarce su da su mika duk wani aiki da mukamai ga mataimakan su.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano (KIRS), Alhaji Sani Abdulkadir Dambo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa daga ofishin sa.

Ya kara da cewa, “A ci gaba da kokarin da ake yi na cimma manufofin gwamnati mai ci, an umurce ni da in sanar da ku cewa an sauke daraktocin, kuma za su mika takardun aikinsu ga mataimakansu nan take.

A cewar sanarwar, daraktocin sassan da abin ya shafa sun hada da

Darakta Muhammad Kabir Umar; Daraktan Ma’aikata, Kabiru Magaji; Daraktan Kasuwanci Ibrahim Sammani; Aminu Umar Kawu, Daraktan Muhd Auwal Abdullahi, Daraktan Binciken Haraji

Ta kara da cewa sauran daraktoci sun hada da Abubakar Garba Yusuf, Daraktan ICT, Hamisu Ado Magaji, Daraktan PAYE, da Bashir Yusuf Madobi, Daraktan Legal & Enforcement.

Solacebase

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *