Hukumar UBEC ta fara aiwatar da shirin inganta ilimin bai daya ga makarantu 111

Screenshot 20240702 160937 Chrome

Gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shirin inganta karatun bai daya a fadin makarantu 111 na kasar nan.

Alfijir labarai ta ruwaito shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta UBEC, Dakta Hamd Bobboyi, ne ya sanar da fara shirin a jiya Litinin a birnin tarayya Abuja a wani taron kwana guda tsakanin UBEC da hukumomin kula da ilimin bai daya na jihohi da kuma shugabbannin shirin inganta ilimin.

Bobboyi, wanda ya samu wakilcin mataimakin babban sakatare na hukumar, Farfesa Bala Zakari, ya yi nuni da cewa an samar da shirin inganta makarantun ne a wani bangare na kokarin hukumar wajen magance kalubalen da ake samu a fannin koyo da koyarwa da kuma yaran da basa zuwa makaranta.

Sannan ya ce zai taimakawa daliban Najeriya da ilimin da ake bukata a matakin farko da kuma kayayyakin aiki da zasu bukata a yayin da ake karni na 21.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *