Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Fara Binciken Almundahanar Tallafin Sana’a A Kano

Screenshot 20240609 230747 Facebook

Hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fara binciken sama da faɗi a cikin shirin tallafawa masu sana’ar a bakin tituna da aka ƙaddamar kwanan nan.

Alfijir labarai ta rawaito shirin wanda ke da nufin baiwa masu sana’a 465 Naira 50,000 kowannensu, amma rahotanni suka bayyana cewa wasu mutane sun yi shigar kura da fatar Akuya a matsayin wadanda suka ci gajiyar tallafin.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda ake gabatar da wasu mutane masu da’awar suna cikin waɗanda aka ware don ba wa tallafin.

Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya tabbatar da gudanar da binciken a yau Lahadi, inda ya ce hukumar za ta tabbatar da hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.

Ya bayyana cewa ana gudanar da binciken ne a ƙarƙashin sashe na 21, 22, da 23 na dokar hukumar, wanda ya shafi ayyukan damfara da karkatar da dukiya.

Rimingado ya jaddada cewa binciken ba wai akan wasu mutane ne aka yi niyya ba amma wani bangare ne na ƙoƙarin da ake na binciko ayyuka daga gwamnatocin baya da na yanzu.

Muhuyi ya yi kira ga jama’a da su bayar da duk wasu bayanansu da kara karfafa gwiwar ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *