Hukumar Yaki da Cin Hanci Ta Kano Ta Karbo Motocin Gwamnati Daga Kwamishinonin Da Suka Ajiye Aiki

IMG 132810 27226 1772195311304

Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Kano ta Karbo motocin gwamnati daga hannun wasu kwamishinoni da suka yi murabus daga majalisar zartarwa ta jihar.

An gudanar da aikin kabar motocin ne a ranar Alhamis ta hannun jami’an hukumar, bayan da aka ce tsofaffin kwamishinonin sun ki mayar da motocin gwamnati duk da rokon da aka yi musu sau da dama.

Mutanen da abin ya shafa sun hada da Air Vice Marshal Ibrahim Umar (mai ritaya), tsohon Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida; Mustapha Rabiu Kwankwaso, tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni; Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha; Dr. Adamu Aliyu Kibiya, tsohon Kwamishinan Harkokin Jin Kai; da Nasiru Sule Garo, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman.

Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, wanda ya jagoranci aikin, ya bayyana wa ’yan jarida cewa dole ce tasa aka dauki matakin, domin tsofaffin kwamishinonin sun ki bin umarnin gwamnati na mayar da dukiyar gwamnati.

Ya ce ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya shigar da korafi kan yadda aka ci gaba da rike motocin gwamnati, tare da bukatar a mayar da su bayan murabus.

Yahaya ya kara da cewa bincike ya nuna wasu daga cikin kwamishinonin sun sayar da motocin gwamnati bayan barin ofis.

“Dukiyar gwamnati ba ta zama mallakar mutum ba. Da zarar jami’i ya bar ofis, dole ne ya mayar da duk motocin gwamnati da sauran dukiyar da ke hannunsa nan take,” in ji shi.

Ya bayyana cewa hukumar ta bi matakan doka, ta kuma samu umarnin kotu kafin ta Karbo motocin.

A cewar Yahaya, an karbo motocin gwamnati guda biyar daga hannun kwamishinoni biyar, amma biyu kacal daga cikinsu su ne motocin asali da gwamnati ta saya. Sauran uku ba su daidai da na asali, domin an sayar da su aka maye gurbinsu da wasu.

Shugaban hukumar ya musanta zargin cewa matakin yana da nasaba da siyasa, yana mai cewa aikin ya yi daidai da nauyin hukumar na kare dukiyar jama’a.

“Ba batun cin zarafi bane, batun kare dukiyar al’ummar Kano ne. Ba za mu lamunci duk wani rashin gaskiya ko rike dukiyar gwamnati ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.

Ya kuma gargadi sauran jami’an gwamnati cewa hukumar za ta ci gaba da sanya idanu kan yadda ake amfani da dukiyar gwamnati, tare da daukar mataki ga duk wanda aka samu da laifi.

A gefe guda, wani tsohon babban jami’in gwamnati, Mohammad Tukur, ya bayyana cewa babu wata doka da ta ba kwamishina damar rike motar gwamnati bayan barin ofis.

Ya ce motocin gwamnati ana ba kwamishinoni ne kawai domin gudanar da ayyukan ofis, ba mallakar su ba.

“Babu wata doka da ta ba kwamishina damar rike motar gwamnati bayan kammala wa’adin aiki, ko an tsige shi ko ya yi murabus,” in ji Tukur.

Sai dai ya ƙara da cewa gwamna na da ikon yanke hukunci na musamman idan ya ga dama ya bar wa wani jami’i mota bayan barin ofis.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *