Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Asabar, 16 ga Janairun 2027, a matsayin ranar gudanar da Zaɓen Shugaban Ƙasa da Majalisar Tarayya.
Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya ƙara da cewa, za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2027.
INEC ta ce ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samun maita ga ƙorafin da wasu ke yi game da jaddawalin zaɓen 2027 da ta fitar, wanda ya nuna za a yi zaɓen a cikin azumi.
A makonnin bayan nan ne INEC ta bai wa ’yan Najeriya tabbacin cewa a tsaye take domin ganin ta yi la’akari da buƙatun kowanne ɓangare na al’umma wajen tsara ayyukan ta.
A farkon watan nan ne hukumar zaɓen ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisar dokokin tarayya a ranar 20 ga watan Fabarairun 2027, yayin da na gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jihohi zai gudana a ranar 6 ga watan Faburairun 2027.
Sai dai sanarwar hukumar zaɓen ta bar baya da ƙura, inda wasu ’yan Najeriya musamman musulmai suka bayyana damuwa kan yadda jadawalin na INEC ke nuna cewa zaɓen zai gudana ne a lokacin azumin watan Ramadana na baɗi.
Masu wannan damuwa na ganin cewa hakan zai shafi musulmai ta la’akari da yadda wasu za su gaza jure fita kaɗa ƙuri’a cikin yanayi na azumi, da kuma yadda yanayin zai iya shafar ƙwazon ma’aikatan INEC da za su kasance cikin azumin lokacin.
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t