Hukuncin Kotu: Kwankwaso ne ya siyar mana da kujerar gwamna ga APC – In Ji Abass

“Muna so mu yi amfani da wannan hanya domin mu gargade shi, da ya nisanta kansa daga jam’iyyar NNPP, ba ma son cin amana a jam’iyyarmu,

Alfijir Labarai ta rawaito wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Alhaji Abass Onilewura, ya zargi tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Kwankwaso da alhakin hukuncin gwamnan Kano, Yusuf Abba, a kotun sauraron kararrakin zaben jihar.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Onilewura a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa Kwankwaso ya sayar da NNPP ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki domin yin shawarwarin neman kujerar minista a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Ya kuma jaddada cewa tsohon dan takarar jam’iyyar NNPP na da hannu a ayyukan kin jinin jam’iyyar ne ya janyo babbar hasarar da jam’iyyar ke fuskanta na ayyana hukuncin kotun a Kano.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Wannan rashin babban abu ne a gare mu a jam’iyyar NNPP, kuma hakan ya faru ne saboda son kai da Kwankwaso ya yi wanda ya sayar da jam’iyyar.

A yayin da muke jiran Tabbataccen Kwafin Gaskiya na Hukuncin Kotun, yana da kyau duniya ta san cewa hakan ba zai faru ba, da Kwankwaso ya bari a yi adalci kuma ya ba wa wanda ya cancanta tikitin takara.

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa ci gaba da huldar Kwankwaso da APC a wani lokaci ya ba su damar gano matsuguni da aka yi amfani da su wajen yi wa gwamnan Kano nasara a kan ‘yan adawa.

“Abin takaici ne yadda wasu daga cikinmu suka yi kokarin kai jam’iyyar inda take a yau, sai dai wani kamar Kwankwaso ya zo ya mayar da duk kokarinmu a banza. Muna farin ciki da an kori wani irin wannan daga wannan babbar jam’iyya.

“Muna so mu yi amfani da wannan hanya domin mu gargade shi da ya nisanta kansa daga jam’iyyar NNPP, ba ma son cin amana a jam’iyyarmu, kuma za mu yi duk abin da zai yiwu don kare jam’iyyarmu daga ‘yan fashin da suka fi damuwa da son rai.

“Zan kuma yi kira ga mambobinmu a fadin kasar nan da su kwantar da hankalinsu saboda sabon shugabanci ya mamaye jam’iyyar, kuma za mu yi duk abin da zai dawo da martabar jam’iyyarmu. Jam’iyyar NNPP za ta fito ta zama babbar murya da adawa da za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci, daidaito da kuma shugabanci na gari.”

Vanguard

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

2 Replies to “Hukuncin Kotu: Kwankwaso ne ya siyar mana da kujerar gwamna ga APC – In Ji Abass

  1. Abubuwa dai sunata Shan babban , musamman daga cikin gida indaa rigingimu suke ballewa daga Mahukunta it’s jamiyyar NNPP

  2. sha sha shi kudi ko mukami ke gabansa,amma kwankwaso ya wuce kanka,wai ma kai waye a jam,iyyar,kuma gaya wa duniya kansila da jam,iyyar Ku ta taba samu,banda shigowar kwankwaso,kai dai da aka baka na cefane ka batawa kwankwaso suna kaje can Ku karata kai da wadanda suka baka kudin,in yau kwankwaso yace mu fita ko kujera Daya baza a samu ba,tarihin jam,iyyar ma sai ya goge

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *