Ibtila i! Mutane biyu sun mutu, 77 sun jikkata a fashewar da ta faru a Ibadan

IMG 20240117 105806

Gwamnan jihar Oyo, a kudancin Najeriya, Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu mutane 77 suka jikkata a wata fashewar da ta faru a ranar Talata da yamma.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin kula da duka wadanda suka jikkata kuma suke samun kulawa a asibiti.

Makinde ya kara da cewa kuma su samar da matsuganai na wucin- gadi ga mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon al’amarin.

Gwamnan wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru a Bodija da ke Ibadan babban birnin jihar ya ce, bayanan farko daga jami’an tsaro sun bayyana abun da ya janyo fashewar.

Inda ya kara da cewa wasu masu aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne da ke zaune a wani gida a wurin suka ajiye abubuwa masu fashewa, kuma su ne suka haddasa fashewar.

Hotunan lamarin da ke yawo a dandalin sada zumunta sun nuna yadda fashewar ta shafi gidaje da motoci da kuma nisan wurin da fashewar ta shafa.

Hukumar kai agajin gaggawa ta NEMA tace an tura ma’aitakai kai dauki da jami’an tsaro, jami’an kashe gobara, jami’an hukumar civil defence da sauransu, domin ayyukan ceto a wurin da lamarin ya auku.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *