Mun dawo daga rakiyar gwamnatin Tinubu – Majalisar Shari’ar Musulunci

FB IMG 1695936417739

Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda ta ce an yi watsi da muradun Musulman ƙasar.

Alfijir labarai ta rawaito Majalisar ta bayyana haka ne a wajen taron da ta kira na kwanaki biyu a Abuja domin nazari kan abubuwan da suka biyo bayan zaɓen 2023 a Najeriya.

Babban magatakardar majalasar, Nafiu Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa majalisar ta kira taron ne saboda sauraron ƙorafe-ƙorafe na ɓangarori daban-daban da mutane ke da shi sakamakon abubuan da suka biyo bayan zaɓen 2023 a Najeriya.

‘Mu ne muka yi jagorancin tattara ƙungiyoyin Musulmi da malamai don su goya wa tikitin da ya kai wannan gwamnatin ga samun nasara, kuma malamai da ƙungiyoyin addini yanzu suna fitowa suna cewa an kai su an baro, an yi ‘Muslim-Muslim tiket’ amma an yi watsi da muradin Musulmi da waɗanda suka sha wahalar zaɓen gwamnatin’. In ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *