Maharan sun yi musayar wuta da sojojin na sa’oi uku kafin su fi ƙarfin sojojin, a cewar mazauna yankinImage caption: Maharan sun yi musayar wuta da sojojin na sa’oi uku kafin su fi ƙarfin sojojin, a cewar mazauna yankin
Alfijir labarai ta rawaito Mazauna ƙauyen mahuta a jihar katsina a arewa-maso-yammacin Najeriya na tserewa daga gidajensu bayan wasu mahara sun auka wa wani sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Batsari.
Masu ɗauke da makaman fiye da ɗari sun kuma cinnawa motoci wuta a sansanin sojin, sannan suka bincike wurin gaba-ɗaya.
Sansanin sojin na ɗauke da sojoji da kuma ƴansanda da sauran jami’an tsaro a lokacin da aka kai harin a daren Litinin.
Jaridar Premium Times ta ambato wata majiya da ke cewa maharan sun ƙona motocin soji guda biyu, amma babu wani jami’in sojin da ya rasa ransa a lamarin.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa masu ɗauke da makaman sun je yankin ne a kan babura da kuma wata babbar mota, sannan sun kwashe tsawon sa’oi uku suna bata-kashi da sojojin, kafin su ci ƙarfinsu.
Haka kuma bayan harin kan sansanin sojin ne suka faɗa wa kauyen na Mahuta suka farfasa shaguna da gidaje suka kwashe kayan abinci da dabbobi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Harin ya janyo tashin hankali a tsakanin mazauna kauyen, lamarin da ya sa suka tsere zuwa wasu ƙauyukan maƙwafta domin su tsira da rayukansu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Gungun masu ɗauke da makamai da ƴan fashin daji da ke satar mutane domin neman kuɗin fansa sun kashe ɗaruruwan mutane a ƙasar, duk da yunƙurin da sojoji suka ce suna yi na magance matsalar.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl