Wani jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari, inda wasu daga cikin kacar sa suka kwace suka fadi.
Har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata ba.
An riga an tura jami’an ceto da na tsaro zuwa wurin da hatsarin ya faru.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya kwace ne bayan ya kasa shiga hanyar da ta dace, inda bidiyo ya nuna fasinjoji suna ta neman mafita a gefen layin dogo.
A cikin wata sanarwa, Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Sanarwar, wacce Babban Daraktan NRC, Kayode Opeifa ya sanya wa hannu, ta ce:
“NRC na tabbatar da hatsarin kwacewar jirgin kasa mai nufin Kaduna (AKTS), da misalin karfe 11:09 na safe, a kan KM 49 tsakanin tashar Kubwa da tashar Asham.”
“Hukumar ta riga ta tura jami’an ceto, ma’aikatan jinya, tare da kusa da asibitoci don bada agaji cikin gaggawa.
“Dukkan jami’an tsaro suna wurin, kuma ana cigaba da aikin mayar da dukkan fasinjojin jirgin lafiya zuwa Abuja.


Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t