Ibtila’i ! Ana zargin wani matashi da yanka wani ladani a masallaci cikin garin Kano

FB IMG 1765809781140

An yi zargin wani mutum da yanka wani  Ladani mai suna Malam Zubairu a Masallacin Yusuf Garko da ke yankin Maraba a unguwar Hotoro da ke birnin Kano wanda ya yi sanadiyar rasa ransa.

Wasu ganau sun ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Litinin, inda wanda ake zargin ya yanka Ladanin lamarin da ya fusata al’ummar yankin.

An zargin wasu mazauna yankin dai, sun bi wanda ya aikata lamarin tare da kashe shi.

Sai dai a martanin da ta mayar rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce ta fara bincike kan lamarin.

Inda ta bayayana cewa  an dawo da zaman lafiya a yankin bayan tura jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da CSP Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano ya fitar.

A cewar ’yansanda, tawagar bincike ta gano makogwaron mamacin a cikin aljihun wanda ake zargin.

Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin tabbatar da an hukunta duk wanda ke da hannu a ciki.

For advertisement or further advisory services, the public has been directed to contact +2348032077835.

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news Fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *