Ibtila’i! Jirgin sama mai saukar ungulu na NAF ya yi hatsari a Fatakwal

FB IMG 1701431352542

Rundunar sojin saman Najeriya NAF ta sanar da cewa jirginta mai saukar ungulu kirar MI-35P ya yi hatsari a Fatakwal, jim kadan da tashinsa.

Alfijir labarai ta rawaito Hadarin ya afku ne da misalin karfe 7.45 na safe jim kadan bayan da jirgin ya tashi domin yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa a Rivers.

Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar ranar Juma’a a Abuja, ya ce ma’aikatan jirgin biyar na cikin jirgin.

Sai dai ya ce dukkan mutanen biyar sun tsira da kananan raunuka kuma suna jinya a cibiyar kula da lafiya ta NAF da ke Fatakwal.

“A halin yanzu shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Hasan Abubakar yana kan hanyarsa ta Fatakwal domin duba halin da ma’aikatan ke ciki, ya kuma duba lafiyar ma’aikatan tare da bayar da wasu umarni.

“Hatsarin wannan yanayin ya sake zama abin tunatarwa game da hatsarin da ke tattare da tukin soja da kuma hadarin da matukan jirgin NAF da masu fasaha ke fuskanta a cikin manyan ayyukansu na kare al’ummarmu da kuma dakile masu aikata laifuka daga munanan ayyukansu,” in ji Gabkwet.

NAN

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *