Ibtila’i! Koƙarin tsere wa ƴan bindiga Mutum 16 sun rasu a haɗarin kwale-kwale a Zamfara

IMG 101605 31825 1756631792330

Ana ci gaba da ƙoƙarin nemo gawarwakin mutanen ƙauyen Dan-Maga da haɗarin kwale-kwale ya rutsa da su a wani kogi, yayin da suke ƙoƙarin tsere wa harin ƴanbindiga a yankin ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Ya zuwa yanzu dai an gano gawar mutum goma sha shida, kuma har an yi jana’izarsu.

Waɗanda kuma suka tsira da rayukansu suna can suna zaman gudun hijira a garin Nasarawar Kifi.

Haɗarin ya auku ne a kogin da ke tsakanin Dan-Maga da Nasarawar Kifi a cewar Bashiru Goga Ƴankifi, mazaunin Nasarawar Kifi wanda a tattaunawarsa da BBC ya ce, “Muna cikin jimami da kaɗuwa sosai bisa wannan iftila’i. A ranar Juma’a da daddare aka gano mutum 14, sai kuma a ranar Asabar aka sake gano mutum 2,” in ji shi, inda ya ce jimilla yanzu sun gano gawarwkin mutum 16 ke nan.

Sai dai ya ce har yanzu mutanen da suka tsira suna ci gaba da gudun hijitra ne saboda suna tsoron komawa yankinsu kasancewar ƴanbindigar na nan a cikin daji.

Shi ma Mustapha Ahmad Gumi ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce “ɓarayi ne suka watsa mutane sai suka zo tsallake kogi, amma sai suka yi yawa a jirgin ruwan kuma yawanci mata ne da ƙananan yara, wanda hakan ya sa jirgin ya kife.”

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *