Ibtila’i! Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

FB IMG 1703458491015

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a ranar Asabar a wani hatsarin mota a garin Kwanar Gujungu da ke karamar hukumar Taura na jihar Jigawa.

Alfijir labarai ta rawaito mai magana da yawun Æ´an sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, a yau Lahadi.

Shiisu ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe 12:00 na rana, inda motoci biyu, kirar Honda saloon mai lamba NSR 469 AE, da wata motar Golf mai lamba AUY 292 XA suka yi karo da juna.

Ya ce motar Honda na É—auke da fasinjoji biyar, sai direbanta mai suna Abdullahi Muhammad, yayin da motar Golf kuma ke É—auke da fasinjoji huÉ—u, da direban Safiyanu Mamu.

Ya ce tawagar ma’aikatan hedikwatar ‘yan sanda ta Taura sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin garin Taura, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

Kwamishinan Æ´an sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, a madadin sauran jami’an rundunar, ya miÆ™a ta’aziyyarsa ga iyalan waÉ—anda suka rasa Æ´an uwansu tare da addu’ar Allah ya gafarta musu.

IMG 20231222 WA0078
IMG 20231222 WA0078

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *