Ibtila’i! Mutum Bakwai Sun Mutu Sakamakon Hayaƙin Janareto

IMG 20240311 WA0055

Mutum bakwai sun mutu sakamakon hayaƙin janareto da ya mamaye ɗakin da suke kwance a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Alfijir labarai ta rawaito an samu gawarwakin mutanen galibinsu ɗaliban Jami’ar Neja Delta a cikin ɗakin Kiɗe-kiɗe watau ‘studio’ ranar Talata da safe, bayan sun shaƙi hayaƙin injin.

Jaridar Punch ta ce sutudiyan na ɗaya daga cikin mutanen da suka mutun ne.

An ce a ranar Litinin da daddare ne marigayan suka fara aiki a sutudiyan, sai barci ya ɗauke su sakamakon gajiyar da suka yi, ba tare da sun kashe injin ba.

Ko da gari ya waye ranar Talata, sai aka samu gawar mutum shida daga cikinsu, yayin da ɗayan ke cikin mawuyacin hali inda nan take aka garzaya da shi asibiti, kafin shi ma ya rasu a asibitin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/F9mRRuOf58G3MlLKsNCJbL

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *