Ibtila’i! Shaguna 180 Ne Suka Ƙone A Wata Gobara Da Ta Tashi A Kasuwar Gandu Sokoto

Screenshot 20240318 124345

Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar jihar Sokoto da safiyar yau Litinin ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.

Alfijir labarai ta rawaito Garba Muhammad Gwazi, shugaban ƴan mashin reshen jihar ya shaida  cewa gobarar ta laƙume shaguna ‘180’ na masu sayar da mashin.

A cewarsa, har yanzu ba a san abin da ya janyo tashin gobarar ba da ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira. Sai dai ya ce gobarar ta soma ne daga wata shara da aka tara.

Ya bayyana cewa gobarar ba ta kai ga asarar rai ko jikkata ba.

Gwazi ya kuma yi kira ga gwamnati ta kai masu ɗauki domin “kasuwancinmu ya miƙe ya ci gaba.” in ji shi.

Shi ma Honarabul Ibrahim Muhammad Giɗaɗo, mai bai wa gwamna shawara kan babbar kasuwar ya ce wutar ta tashi da sanyin safiyar yau.

Ya ce “ɓangaren da ya ƙone sosai a cikin kasuwar shi ne na ƴan mashin da kekuna, ana iya samun shago guda ɗauke da mashin fiye da 200 ko 100, shagunan gaba ɗaya sun ƙone,”

“Waɗannan mashina akwai waɗanda suka haura miliyan, akwai asara mai yawa.” ya ƙara da cewa.

Giɗaɗo ya ƙara da cewa jami’an kashe gobara sun kashe kashi 80 cikin 100 na gobarar da ke ci

Radio Nigeria Kaduna

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *