Ibtila’i! Wani Gini Ya Rushe Tare Da Kashe Mutane Wasu Kuma Sun Jikkata A Kano

Rushau

Wani bene mai hawa biyu yayi sanadin mutuwarwasu mutane guda biyu, yayin da wasu biyu suka jikkata a Jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito ya rushe ne da misalin karfe 2 na darenjiya Laraba a unguwar Nomansland dakekaramar hukumar Fagge, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi.

Ambaliya ce ta biyo ta bayan daukewar ruwan sama da akayi, wanda yayi sanadiyar rushewar benen, kamar yadda kakakin Hukumarkashe gobara ta jihar Kano Samunu Abdullahi, ya bayyanawa manema labarai a yau Alhamis 05,ga Satumba,2024.

Saminu, ya ce an garzaya da wadanda aka ceto daga benen da ya rushe zuwa asibiti, inda a halin yanzu suke samun kulawa.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *